Ra’ayi: Dalilan da zasu sa Kanawa su zabi Gawuna da Garo

Date:

Daga: Aminu Dahiru

 Tun bayan da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya yi rawar gani a muhawarar da BBC Hausa ta shirya a Kano a yan makonni da suka gabata, na gana da wani babban jigo a jihar nan, inda muka tattauna kan makomar jihar kano bayan kammala zaben gwamna dake tafe .
 Tattaunawar ta kasance mai matukar amfani wadda muka shafe sama da sa’a guda, inda jigon ya yi min bayani dalla-dalla, kan dukkan man ‘yan takarar gwamna a jihar kano, ya kuma dora kowannen su a sikeli daidai da abun da yake shirin yiwa kano idan ya zama gwamna.
Talla
 Batun da ya dauki lokaci mai yawa shi ne yadda kowanne dan takarar zai samu karbuwa a wajen al’umma daidai da tarihin sa, da kuma gogewar kowanne su.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
Jihar Kano wuri ne da masu mutane suke zabar wanda suke so, Inda  mutumin ya ce kimanin shekaru 24 kenan da aka rika samun sauyin gwamnati daga Kwankwaso zuwa  Shekarau har zuwa gwamnatin Ganduje hakan ya nuna kwarewar masu zabe a kano .
 “Kowane dan takarar yana da Inda yafi  kwarewa , amma Gawuna kwarewar sa ba ta misaltuwa, Saboda yadda ya fara harkar siyasarsa tun daga tushe kamar yadda abokin takararsa Alhaji Murtala Sule Garo ya ke, Inda har ya kai ga matsayin  mataimakin dan takarar gwamnan jihar kano .
 “Na biyu, al’ummar Jihar Kano sun dade da daina zabar yan bani na iya, Kuma ba za su zabi dan takarar da aka kakaba musu ba, wanda kuma bashi da kwarewa son zuciya ne kawai yasa aka tsayar da shi, to wannan lokaci ya dade da wucewa.
 “Na uku, gaggarumin ci gaban da Gwamna Ganduje ya samar a harkar mulki kowa ya gan shi a zahiri, A cikin shekaru bakwai da rabi da suka gabata Ganduje ya sauya kano musamman ta fuskar aiyukan raya kasa da samar da sauran ababen more rayuwa. Kuma  Ma’aikatan gwamnatin jiha na karbar albashinsu a karshen kowanne wata, wadannan Misalai ne na nasarorin da aka samu guda biyu kawai .
 “Na hudu, Kanawa suna da wayo, Babu shakka za su yi watsi da duk wanda ya yi niyyar sake mulkar su ta hanyar sanya wakili. Jama’a sun fara fahimtar cewa tsohon gwamnan jihar na ya baiwa surikinsa takara duk da cewa ba shi da kwarewa kawai don ya rika ta juya dukiyar jihar bayan wa’adin sa ya kare. ”
 Ya ce mutane kano Gawuna da Garo, za su zaba saboda sun sani cewa jihar za tafi zama lafiya a hannunsu.
 Ya kara da cewa Gawuna da Garo Kwararru suna da kishi  kuma suna da niyyar yi wa al’ummar jihar hidima gwargwadon iyawarsu.
 Al’ummar jihar Kano za su kada kuri’arsu ga Dr Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa Alhaji Murtala Sule Garo a ranar 11 ga Maris, 2023 domin samun cikakken cigaba a Kano.
 Aminu Dahiru shi Mataimakin Shugaban kungiyar GGPD kano kungiyar dake yada manufofin Gawuna da Garo a kananan hukumomin 44 dake kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...