Daga Halima Musa Sabaru
Babban bankin Najeriya CBN ya ce yana nan kan bakarsa ta daina amfani da tsofaffin kuɗi na naira 200 da 500 da 1,000 daga 31 ga watan Janairu.
Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ne ya tabbatar da hakan a yayin wani taro da CBN ɗin ya yi a ranar Talata.
Sai dai duk da tsawon lokacin da CBN ɗin ya bayar na daina mayar da kuɗin banki, amma har yanzu akwai jama’a da dama musamman ma waɗanda ke a karkara waɗanda ba su mayar da kuɗaɗen banki ba.

Akwai bankuna da dama a faɗin Najeriya da ana nan ana layi domin mayar da kuɗaɗen.

Ko waɗanne hanyoyi jama’a za su bi idan suna son karɓar sabbin kuɗi su mayar da tsofaffi?
Bankuna
Jama’a za su iya zuwa bankuna da ke kusa da su domin mayar da tsofaffin kuɗi.
Sai dai ko da mutum ya je banki, ba za iya ba shi kuɗin da suka wuce dubu ashirin na sabbin kuɗi ba a rana.
Haka kuma mutum zai iya samun sabbin kuɗin ne kawai ta na’urar ATM.
Babban bankin CBN dai ya tabbatar da cewa ko nawa mutum yake da shi na tsofaffin kuɗi zai iya kaiwa banki domin su kasance a cikin asusun ajiyarsa, idan ya so ya rinƙa zarar kuɗinsa a hankali.
A kullum mutum zai iya cirar dubu ashirin ne sa’annan a duk mako kuma kuɗin da mutum zai iya cira lakadan ba za su wuce dubu 100 ba.
Wakilan babban banki na musamman
Babban bankin Najeriya CBN ya samar da wakilai na musamman ko agent-agent fiye da miliyan guda a fadin Najeriya da suke aikin sauyin kuɗi.
Wakilan sun soma wannan aikin ne tun a ranar 23 ga watan Janairun bana.
Babban dalilin da ya sa aka fito da wannan tsarin shi ne sauƙaƙa wa jama’a musamman na karkara hanyoyin da za su bi domin sauya musu kuɗi.
CBN ɗin ya tabbatar da cewa yakan ba kowane wakili sabbin kuɗi a duk mako kimanin 500,000 domin sauya wa jama’a.
Sai dai idan mutum ya je da kuɗinsa ba za a iya sauya masa kuɗin da suka wuce naira dubu goma ba.
Misali idan mutum ya je wurin wakilai masu sauya kuɗi da kuɗaɗe masu yawa, taimakon da za su iya yi mashi shi ne su karɓi kuɗin sa’annan su buɗe masa asusun ajiya, amma za su iya ba shi naira dubu goma sabbi.