Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mai ba gwamnan Kano Ganduje shawara Kan cigaban al’umma da manufar gwamnati Kabiru Inuwa Hayinhago, ya nuna damuwar da ya ke ciki Kan kama Dan uwansa Tasi’u Audu Sakamakon aikin jam’iya na samunsa da Katukan zabe 26 a wani yunkurin yin tallafi ga mata, abin da yanzu haka yana garkame a kurkukun Kurmawa batun da ya ce tun daga lokacin da aka kama shi har yanzu ba ya iya samun bacci saboda bacin rai kan abin da ya faru na nuna halin sakaci da ko in kula daga mahukunta.
Cikin wata takarda da ya rabawa manema labarai ya ce Hakan abin takaici ne da Yakamata sauran Yan jam’iya su yi karatun ta nitsu, wajen nisantar duk wani aiki da wani zai za su domin neman biyan bukatarsa, in da ya Kara da cewa yanzu haka alummar Garin Hayinhago dake karamar hukumar Dawakin Tofa, su na shirye shirye na daukar matakin nemawa dansu hakki Kan abin da aka saka shi Amma aka gaza Samar masa da wata mafita na fitar da shi daga kangin rayuwa.
A karshe Hayinhago ya ce har yanzu ba wata tawaga da aka tura wajen iyalan Malam Tasi’u domin jajantawa abin da ya kira rashin tausayi da rashin sanin darajar Dan jam’iya.
Idan za’a iya tunawa dai kadaura24 ta rawaito an kama wani da katin zabe har guda 26 a karamar hukumar Dawakin Tofa wanda kuma tuni aka turashi gidan yari gabanin yanke masa hukunci.

