Daga Abdulrashid B Imam
Majalisar dattijai ta bukaci babban bankin Najeriya CBN ya kara wa’adin cire tsoffin kudaden Naira daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Yuli.
Kadaura24 ta rawaito Majalisar ta kuma bukaci CBN da ya samar da wata dama bude ga mutanen da ba su da asusun ajiyar banki ta yadda zasu sauya kuɗin nasu cikin sauki .

Wannan kiran na majalisar dattijai ya biyo bayan kudirin da Sanata Sadiq Suleiman daga jihar Kwara ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talata.

Da yake gabatar da kudirin, Suleiman ya tunawa ya majalisar cewa majalisar dattijan a kudurin ta na ranar 28 ga watan Disamba, 2022, ta bukaci CBN da ta kara wa’adin amfani da tsofaffin kudin daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa 30 ga watan Yuni.
Ya ce duk da haka, babban bankin ya dage kan dakatar da amfani da tsoffin takardun kudi na naira nan da karshen watan nan naJanairu.
Suleiman ya koka da cewa babu isassun sabbin kudaden a cikin jama’a, don haka ya bukaci a tsawaita ranar zuwa ranar 31 ga watan Yuli.
Ya ce: ” A duk faɗin duniya daukar irin wannan matakin na bazata idan ba ai hankali yana haifar da hargitsi a cikin al’umma.
“Ya kamata majalisar dattawa ta tsawaita amfani da tsoffin kuɗaden zuwa ranar 31 ga Yuli,” in ji shi.