Wasu daga cikin fadawan Shehun borno sun kone kurmus

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa ta tabbatar da cewa wani hatsarin mota ya rutsa da rayukan wasu fadawan Shehun Borno guda uku, Alhaji Abubakar Umar Ibn Garbai El-kenmi, a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Kwamandan Hukumar a jihar ta Borno, Utten Iki Boyi, ya shaida wa Jaridar Daily Trust a Maiduguri da safiyar ranar Talata cewa mutane shida ne suka yi hatsarin wanda ya afku a ranar Litinin, amma an ceto uku, inda aka kai su wani asibiti da ke kusa.

Talla

A cewarsa, lamarin ya faru ne a kusa da yankin Benisheik lokacin da motar ta yi dungure sannan ta kama da wuta.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Ya ce nan da nan suka tura jami’an su zuwa wajen da lamarin ya faru, inda aka samu mutum uku sun ƙone kurmus har ba a iya gane su.

Sai dai ya ce an samu nasarar ceto mutum uku inda aka kai su zuwa babban asibitin Beneshiek don yi musu magani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...