Jami’ar Bayero ta Musanta Karin Kudin Makarantar ga Dalibai

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

 

Hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero ta Kano ta karyata rahoton da ke cewa jami’ar ta kara kudin makaranta.

 

A wata sanarwa da mataimakin magatakardar mai kula da harkokin jama’a Malam Lamara Garba ya raba wa manema labarai a Kano, ya ce labarin da aka yada bashi da tushe ballantana makama.

Talla

Sanarwar ta ce, “An jawo hankalin Hukumar Gudanarwar Jami’ar Bayero ta Kano game da wata wasika ta bogi da ake yadawa a shafukan sada zumunta inda ta sanar da karin kudaden makaranta.”

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

“Bisa la’akari da abubuwan da suka gabata, ya kamata dalibai da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki su lura cewa har yanzu Jami’ar Bayero ba ta yanke shawara kan karin kudin makaranta ba, sabanin yadda wasu marasa kishin al’umma suke yada labaran karya a shafukan sada zumunta.

 

Sai dai sanarwar ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da bayanan da ake yadawa su dauke su a matsayin labaran na bogi .

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...