An tura mutumin da aka kama da katunan zaɓe guda 29 zuwa gidan Yari a Kano

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Wata kotun majistare a Kano, karkashin jagorancin mai Shari’a Jostis Mustapha Sa’ad Datti, ta tura da mutumin nan mai suna Tasiu Abdullahi Hayin Hago, zuwa gidan ajiya da gyaran hali, sakamakon rashin cika ƙa’idar beli.

 

Jami’an yan sanda ne suka samu nasarar cafke Tasiu Abdullahi mai shekaru 45, tare da katunan zaɓe na din-din-din (PVC) guda 29, wadanda dukkansu mallakin mutanen karamar hukumar Dawakin Tofa ne a jihar Kano, inda ya bayyana cewa, Abba Ganduje ne yake sa shi ya karɓo.

Talla

Mai Shari’a ya dage cigaba da sauraron Shari’ar, har zuwa ranar 30 ga watan da muke ciki na Janairu, tare da umarnin a cigaba da tsare shi a gidan ajiya da gyaran hali.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...