Inganta aikin lafiya: Ɗalibai kusan 200 sun kammala makarantar koyon aikin jinya da ungozoma a kano

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Makarantar koyar da aikin jinya da ungozoma dake jihar kano ta gudanar da da bikin yaye dalibai karo na biyu su kimanin 197 wadanda suka fito daga makarantun gwarzo, Dambatta da kuma jihar kano.

 

Shugabar makarantun Dr. Mairo Sa’id Muhammad ta bayyana cewa makarantun suna bada gagarumar gudanmawa wajan samar da kwararrun ma’aikatan jiya da ungozoma a fadin jihar Kano da kasa baki daya.

 

Makarantun suna bada gudunmawa wajen shawo kan matsalolin da mata suke fuskanta a lokutan goyan ciki da kuma haihuwa, domin samun al’umma ta gari.

 

A nata bangaren Shugabar makarantar dake kano Hajiya Munubiya Abdullahi ta bukaci daliban da suka kammala wannan karatun dasu kasance wakilai na gari a duk inda suka sami kansu, daga bisani ta bayyana irin matsalolin da makarantun ke fuskanta wadanda suka hadar da rashin hasken wutar lantarki da matsalar abun hawa a daukacin makarantun, inda ta bukaci gwamnati da ta kai musu dauki.

 

 

Da yake jawabi professor Umar Sani Fagge wanda malam Nazir Adamu ya wakilta, ya bukaci daliban da suka kammala karatun da suyi amfani dashi wajan tallafawa ‘yan uwansu mata musamman wadanda suke zaune a karkara domin magance matsalolin da suke fuskanta a lokutan goyan ciki da haihuwa.

Talla

 

Makarantar ta karrama wasu daga cikin malamai, dalibai da ma’aikatan makarantar wadanda suke yi fice wajan bada gagarumar gudanmawa a bangarori da dama.

 

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Wadanda aka karrama sun hadar da Aisha Salisu gwarzo da malama Rabi da kuma malam Ahmad Ibrahim.

 

 

Wakilinmu ya bamu labarin cewa Taron ya samu halarta al’umma da dama, wadanda suka hadar da shugaban kungiyar kwadago ta jihar kano Kabir Ado Minjibir sai kuma wamban Bichi injiniya sani Abdulkadir da zubairu idris Danbatta da sauran al’umma da dama.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related