Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Wudil da Garko Hon. Engr. Muhd Ali Wudil ya kaddamar da aikin wata hanyar layin gidan alhazai zuwa shagari quarters dake karamar hukumar Wudil, wadda ta shekara talatin da lalacewa.
Kadaura24 ta rawaito yayin da yake kaddamar da aiki Dan majalisar ya ce zai gudanar da aikin ne domin saukaka al’ummar yankin duba da yawan al’ummar da suke amfani da titin a kodayaushe .

Engr. Muhd Ali Wudil yace baza a dauki lokacin Mai tsawo ba ana aikin, Inda ya bada tabbacin tunda aka fara akin titin mai tsahon kilomita guda baza a tsayaba sai an kammala shi domin amfani al’ummar yankin.

” Mun San yadda wannan titi yake da matukar muhimmanci musamman wajen kai marasa lafiya asibiti, da kuma gudanar da harkokin ku na yau da kullum, hakan tasa na gudirci aniyar gyara titin don kuma ku daina Shan wahalar titin, Kuma na tabbata hakan zai inganta harkokin ku na yau da kullum harma da tattalin arzikin wanann yankin”. Inji Dan majalisar
Yace ya ga wannan aikin yanzu haka ma ana gudanar da aikin wasu hanyoyin wadanda suka hadar da titin cikin garin Wudil kofar yamma da Kuma titin indabo zuwa wudil dukkanin su yanzu haka ana aikin Kuma tunda aka fara babu wanda aka tsaya a cikin su.