Muhawarar BBC a Kano: Kwarewa da Nasarar Gawuna ta Kara bayyana – Musa Iliyasu Kwankwaso

Date:

Daga Nura Abubakar Cele

 

 

Dan takarar Dan majalisar tarayya na kananan hukumomin kura madobi da garun Mallam a jam’iyyar APC Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana muhawarar yan takarar gwamnan kano da BBC Hausa suka shirya a matsayin wata hanya data Kara fito da kwarewa da nasarar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.

 

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ganawarsa da jaridar kadaura24.

 

Talla

Yace Dr. Nasiru Gawuna wanda shi ne dan takarar gwamnan kano na jam’iyyar APC, ya kara nunawa duniya irin kwarewar da yake da ita wajen sanin matsalolin Kano, da kuma hanyoyin magance su da kuma yadda zai ciyar da jihar kano gaba idan Allah yasa ya lashe zaben.

 

  • ” Dubi irin amsoshin da ya bayar game da tambayoyin da akai masa, ka da ji kasan kwarewar su ba iri daya bace da ta sauran yan takarar, Kuma hakan ya kara fito da kimar da aiyukan da gwamnatin jihar kano ta gudanar karkashin jagorancin Shugaban mu Dr. Abdullahi Umar Ganduje”. Inji Kwankwaso

 

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

” Wasu daga cikin yan takarar ma fa tambayar da akai musu ba amsarta suka rika bayarwa ba, shi kuwa dan takarar gwamnan jam’iyyar Yan gwari ficewa ma yayi daga dakin muhawarar Saboda bashi da abun da zai fadawa mutane kano, Kuma haka ya nuna ko da ya zama gwamna sai yafi fifita bukatun uban gidansa akan mutanen kano”. Musa Iliyasu Kwankwaso 

 

Dan takarar dan majalisar na kura madobi da garun Mallam a jam’iyyar APC, yace babu shakka ficewar Abba Gida-gida daga wajen muhawarar ya tabbatarwa al’ummar jihar kano cewa bai shirya su zabe shi gwamnan su ba, saboda ya kasa fada musu yadda zai mulke su.

 

Yace al’ummar jihar kano yanzu ya ragewa ranar zabe su fito su zabi Dr. Nasiru Gawuna da Murtala Sule Garo, domin aiwatar da kyawawan manufofin su wadanda yake da yakin zasu kara daga darajar Kano a idanun duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...