Da dumi-dumi: Gobara ta tashi a hedikwatar ‘yan sandan jihar Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

 

Hedkwatar ‘yan sandan Kano da ke Bompai a karamar hukumar Nasarawa, tana cin wuta, inda ake zargin ta kona ofisoshi da muhimman bayanai da dama.

 

 

Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce tuni ta tura jami’an ta wurin da lamarin ya faru domin dakile gobarar da ta tashi a ginin bene mai hawa daya na rundunar.

 

Talla

Rahotanni da basu tabbata ba sun nuna cewa gobara ta tashi ne a saman benen, Inda ta kama ko’ina amma banda ofishin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

 

Ko da kadaura24 ta tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ta wayar hannu, mun sami wayarsa a kashe har lokacin haɗa wannan rahoton, amma har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...