Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jiha zamfara ya ce gwamnatinsa ta gano likitocin bogi 199 da ake albashin gwamnatin jihar.
Ya ce gwamnatin jihar tana biyan albashin “likitoci 280 amma akwai likitoci 81 kawai na gaske a jihar .
Matawalle ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a gidansa da ke garin Maradun, hedikwatar karamar hukumar Maradun ta jihar, inda ya kara da cewa lamarin ya sa gwamnatin jihar ta fuskantar mawuyacin halin wajen biyan albashin su na wata-wata.

Ya ce ya gana da jami’an kungiyar kwadago ta kasa NLC reshen jihar da sauran masu ruwa da tsaki kan yadda za a binciko wadancan likitocin bogi guda 199 da suka dauki tsawon lokaci suna karbar albashi ba bisa ka’ida ba da nufin gyara matsalar.

“Masu ruwa da tsakin sun tabbatar min da cewa dalilin da ya sa aka jinkirta biyan albashin ma’aikatan kiwon lafiya shi ne yadda suke son tabbatar da cewa al’amura sun tafi daidai kuma nan ba da dadewa ba za mu magance dukkan matsalolin a bangaren lafiya.
“Na biya albashin watan Nuwamba da Disamba ga dukkan ma’aikatan lafiya amma abin takaici mun gano rashin jituwa kan yadda ake biyan albashin,” in ji Matawalle.