Daga Ibrahim Aminu Riminkebe.
Babbar kotun jihar kano mai lamba 14 dake zaman ta akan titin miler, karkashin jagoranci mai shari’a Justice Jamilu Suleiman ta bada umarnin dakatar da Alhaji Ashiru mai Kada, da Nisa’i Mamuda da kuma Malam Aliyu Kofar Naisa (Mai Aljana), dasu dai na bayyana kan su a matsayin shugabannin kungiyar masu sana’ar magungunan gargajiya ta kasa reshen jihar Kano.
Da yake shigar da koken nasu, ta hannun lauyan bangaran masu kara Barista Yajin Rana ya shedawa kotun cewa wadanda suke karar na yinkurin yiwa dokokin kungiyar karan tsaye, baya ga hana sabbin shugabannin kungiyar gudanar da jagorancin kungiyar.

Barista Yajin Rana ya kara da cewa, tuni shugaban kungiyar masu sana’ar magungunan gargajiya ta kasa ya jagoranci rantsar da sabbin shugabannin kungiyar a matakin jihar Kano karkashin jagoranci Dakta Ibrahim Arba Dan Sokoto dakuma mataimakan sa dake dukkanin masarauta guda biyar na jihar Kano.

Yace, suna bukatar kotun ta bada umarnin dakatar da Alhaji Ashiru Mai Kada da Nisa’i Mamuda dakuma Malam Aliyu Kofar Naisa (Mai Aljana) da Kiran kan su a matsayin shugabannin kungiyar masu sana’ar magungunan gargajiya ta kasa reshen jihar Kano, a sakamakon rashin bin ka’idojin kudin tsarin mulkin kungiyar na zabe ba.
Barista Yajin Rana ya a sake shedawa kotun cewa, an bi dukkanin ka’idojin da kudin tsarin mulkin kungiyar ya shumfuda kafin zabar sabbin shugabannin kungiyar masu sana’ar magungunan gargajiya ta kasa reshen jihar Kano wanda ya gudana a makarantar koyan harshen larabci ta (S.A.S) dake kan titin zuwa fadar mai martaba sarkin Kano.
Lauyan bangaran masu karar ya sake zargin Alhaji Ashiru mai Kada dakuma tagawar sa da yinkurin kawo rudani dakuma rarrabuwar kawunan ‘yayan kungiyar masu sana’ar magungunan gargajiya a matakin jihar Kano.
Daga bisani alkalin kotun justice Jamilu Suleiman ya amunce da rokon bangaran masu gabatar da kara, a inda nan take ya bada umarnin dakatar da wadanda ake karar a matsayin shugabannin kungiyar masu sana’ar magungunan gargajiya ta kasa reshen jihar Kano da wato Alhaji Ashiru mai Kada da Nisa’i Mamuda dakuma Malam Aliyu Kofar Naisa (Mai Aljana).