Daga Aisha Aliyu Umar
Gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jaddada bukatar samun ma’aikata masu kwazo da himma musamman a karshen kowace gwamnati.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci rantsar da wani sabon babban sakatare Alhaji Yusuf Datti Husain a gidan gwamnati.

Ya bayyana cewa akwai bukatar samun irin wadannan jajirtattun ma’aikata masu gaskiya don ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati don samun nasarar mika mulki daga wata gwamnati zuwa wata .
Gwamnan ya bayyana cewa sabon babban sakataren kafin nada shi sai da aka duba dimbin gogewarsa da himmarsa yayin da ya yi aiki a ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu ta jihar kano.

Gwamna Ganduje ya kuma umarci sabon sakataren da ya ci gaba da gudanar da aikinsa bisa gaskiya da jajircewa don cimma manufofin da aka sa gaba.
Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnati M. A Lawal ne ya rantsar da sabon sakataren na Alhaji Yusuf Datti Husain daga karamar hukumar Dawakin Kudu.