2023: Kafin 12 mun kayar da jam’iyyar NNPP, Gawuna ya ci zabe- Faizu Alfindiki

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

A shirye-shiryen da jam’iyyar APC ke gudanarwa na ganin ta samu nasara a zaben shekarar 2023, shugaban karamar hukumar birni da kewaye Hon. Faizu Alfindiki, ya jagoranci taro na musamman na mata zallah  wadanda suka fito daga unguwar marmara.
Comrade Faizu Alfindiki, wanda shi ne shugaban kwamitin matasa na yakin neman zaben dan takarar gwamna na jam iyyar APC , ya bayyana cewar APC ta shirya tsaf domin fafatawa da kowacce jam’iyya la’akari da ingantattun yan takarkarun da aka fito da su, yana mai cewar Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya kasance mafi cancanta a cikin ‘yan takara.
Talla
Alfindiki ya bayyana cewa zaben Gawuna  da Garo zai sake mayar da Jihar kan turbar ci gaba da inganta rayuwar al’umma, inda ya baiwa mata. Da suka. Halarci taron kyautar 200K ya kuma rabawa marayu kayan karatu a yayin taron.
Dan Majalisar Jiha na karamar hukumar birni Hon. Maje Ahmad Gwangwazo, da kuma kakin yakin naiman zaben Gawuna Garo Kano State, Comrade Mohammed Garba  sun yi kira ga magoya bayansu da su zabi  APC a 2023.
Malam Mohammed Garba a yayin taron ya bada kyautar Naira dubu 200 ga matan, yayin da maza suma aka basu Naira dubu 200. Ya bayanna cewa idan aka zabi Gawuna da Garo zasu tallafawa matasa ta ɓangaren samar da ayyukanyi da ababen More rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...