Daga Rukayya Abdullahi Maida
Wata gobara ta tashi da safiyar Talata a unguwar Ebute Metta da ke Legas.
Wani ganau ya shaidawa DAILY POST cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe tara na safe.
Gobarar ta tashi ne a daya daga cikin gine-ginen da ke kan titin Ibadan daura da titin makabarta.

Da karfe 10 na safe, wasu gidaje guda biyu, lamarin da ya shafa da sanya sauran mazauna unguwar cikin firgici.
“Na kira hukumar kashe gobara ta Legas da misalin karfe 9:05 na safe, sun iso bayan mintuna 40, wanda sun dan makara.
Har yanzu jami’an hukumar masu ba da agajin gaggawa suna nan suna kula da wurin, amma sun sami damar shawo kan lamarin yayin da mazauna unguwar ke kirga irin asarar da suka yi.
Lamarin ya biyo bayan gobarar da ta tashi da yammacin ranar Litinin a kan titin Aladelola da ke unguwar Ikosi Ketu a Legas.