Daga Zara Jamilu Isa
Gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ya koka da yadda kwararrun likitoci sama da 170a jihar suka bar aikin gwamnati a cikin watanni ukun da suka wuce .
Da yake jawabi a wajen kaddamar da wata cibiyar kular kula da lafiya ta zamani da aka gina akan kudi Naira miliyan 350 da ke babban asibitin garin Offa a karamar hukumar Offa a jihar Kwara, wanda wata kungiyar ‘yan asalin yankin Offa Metropolitan Club (OMC) suka gina a ranar Asabar, gwamnan ya ce gwamnatin jihar ba zai iya kula da sha’anin kiwon lafiya ita kadai ba.

“Mu a Kwara, muna samun kalubalen yadda likitocn mun suke komawa asibitocin gwamnatin tarayya wasu kuma suna komawa Legas da Abuja, yayin da su kuma na Legas sume komawa kasashen Ingila, Amurka, da sauran kasashen turai. Wannan shi ne ɗayan daga cikin manyan ƙalubalen da muke fuskanta”. inji Gwamnan
Gwamnan wanda ya nuna jin dadinsa kan wannan aiki, ya ce gwamnatin jihar za ta tallafa wa shirin domin amfanin jama’a.
“A cikin watanni uku da suka gabata, mun yi asarar likitoci 170 a ma’aikatan jihar. Wannan yana daya daga cikin kalubalen da kuke da shi; samun kwararrun likitoci a biya su daidai. Adadin da muka rasa na likitoci da ungozoma yana Kara karuwa kullum, Yawancin wadancan likitocin kawai kudi ne a gabansu ba batun kishin kasa a gare su, hakan tasa sai barin jihohi da yawa suna rasa likitoci, ” in ji shi.