Mazauna Amuruka na kwona kayan su sakamakon matsananci Sanyi

Date:

 

Shugabannin al’umma na gargajiyar Amurka a Jihar South Dakota na neman tallafin gaggawa sakamakon dusar ƙanƙara da tsananin sanyi da suke fuskanta.

 

Shugaban ƙabilar Oglala Sioux Frank Star ya faɗa wa BBC cewa ƙanƙara ta lulluɓe gundumarsu ta Pine Ridge, abin da ya sa dukkan kayayyakinsu suka ƙare saboda ba shiga ba fita.

 

Ƙanƙara mai tudun inci 30 na sauka a yankin sannan guguwa ta tara dalar ƙanƙarar mai tudun ƙafa 12.

Talla

Anna Halverson, wakiliyar yankin unguwar Pass Creek a gundumar, ta faɗa wa mujallar Darsha Dodge Rapid City cewa “akwai dalar ƙanƙarar da ta kai tsawon gidaje, wani zubin kamar faɗin yadi 60 zuwa 70”.

 

Ta ƙara da cewa: “Mun ga inda mazauna gundumar ke ƙona tufafinsu a wuta don su ji ɗumi saboda ba su da itace.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...