Daga Maryam Adamu Mustapha
Hukumar Inshora ta Kasa, NAICOM, ta kara kudin inshorar masu ababen hawa na uku daga N5,000 zuwa N15,000 duk shekara daga Janairu 2023.
Sanarwar ƙarin na ƙunshe ne a cikin takarda mai lamba; NAICOM/DPR/CIR/46/2022 ga kamfanonin inshora, mai ɗauke da kwanan wata Disamba 22, 2022.

An yi wa sanarwar lakabi da: Sabon Farashi mai girma na Inshorar Motoci, kuma daraktan Manufofi da Dokoki na NAICOM, Leo Akah ne ya sanya hannu a madadin Kwamishinan Inshorar.
“Bisa aiwatar da aikinta na amincewa da ƙimar kuɗin inshora a ƙarƙashin sashe na 7 na Dokar NAICOM ta 1997 da sauran dokoki, Hukumar ta fitar da wannan da’irar akan sabon farashin inshorar motoci wanda zai fara aiki daga Janairu 1, 2023,” in ji ta.