Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Rundunar Sojan Najeriya ta ce dakarunta sun kashe mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da na ISWAP 103 cikin mako uku da suka gabata.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce dakarun rundunar Operation Hadin Kai ne suka kashe masu iƙirarin jihadin a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Kazalika, ta ce ta kama ‘yan ta’adda 22 da masu taimaka musu 18 yayin samamen da ta kai a wannan tsakanin.

Shekarar 2022 ta zo wa ƙungiyoyin da asara iri-iri, musamman shugabanninsu da aka kashe a Gabas ta Tsakiya da Afirka ta Yamma.
Sai dai su ma sun ƙaddamar da munanan hare-hare kan gidan yari, musamman na Kuje a Abujar Najeriya, inda ISWAP ta fitar da mayaƙanta da kuma ɗaruruwan tsararru.