Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Ma’aikatan da ke karkashin karamar hukumar Bassa a jihar Kogi sun fara kukan neman agaji saboda gazawar gwamnatin jihar wajen biyan su albashin watan Nuwamba.
DAILY POST a cikin wannan rahoto na musamman, ta yi duba ne kan yadda rikicin karamar hukumar Bassa ya jefa ’yan fansho da ma’aikata a kananan hukumomi cikin mawuyacin hali.

Karamar hukumar Bassa dai ta fada cikin rikici tun a shekarar 2016, inda aka kashe mutane da dama, aka lalata gidaje da kuma raba ‘yan asalin yankin da muhallansu, Rikicin dai ya faru ne tsakanin Bassa Komu da Egbira Mozum. DAILY POST ta tattaro cewa kabilun biyu suna takun-saka a tsakaninsu kan takaddama akan kamun kifi.
Gwamnati dai ta kafa kwamitin bincike don duba rikicin amma ba a yi komai ba. Wannan ci gaban ya kara dagula matsalar mutanen da ke aiki a karamar hukumar Bassa.