Daga Rukayya Abdullahi Maida
Masu ababen hawa a jihar Kano suna siyan man fetur akan kudi naira 340 kan kowace lita.
Masu gidajen man dai suna sayar da man ne a kan farashin da aka da suka ga dama, duk da gargadi da hukumar tsaron farin kaya (DSS) na ganin an shawo kan matsalar karancin mai a fadin kasar.
Binciken da aka gudanar a wasu gidajen Mai dake birnin kano ya nuna yadda ake samun dogayen layin motoci.
A wasu gidajen mai da ke kan titin Zoo, Zariya da Maiduguri a cikin birnin Kano, Inda ake da Karan dogayen layin masu ababen hawa ana sayar da man a naira 310 zuwa N340 akan kowace lita.

Duk da haka, wadanda suka sayin man a gidajen man AA Rano, Maikifi da kuma NNPC dake birnin kano, duk da sun kawashe sa’o’i masu yawa sun ce sun sayi man akan N185 zuwa 210.
The Guardian ta rawaito cewa wasu daga cikin gidajen man mai da ke da samfurin za su rufe wuraren su da rana, amma suna rarrabawa da daddare akan farashi mai ban mamaki.
Wasu masu ababen hawa sun ce ba su da wani zabin da ya wuce su sayi man a wajen yan bunburutu don kaucewa dogayen layukan da ake yi a gidajen man.
Wani mazaunin kano mai suna Isa Idris ya zargi dillalan man da laifin haifar da karamcin man .
Sai dai tsohon ma’ajin kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN), Abdullahi Maikifi, ya shaidawa jaridar Guardian cewa dole a dorawa gwammati laifin tsadar man fetur din musamman a Kano.
Ya kara da cewa βyan kasuwar suna kashe kudin jigilar man daga Legas zuwa Arewa duk da hadarin matsalar tsaro da rashin ingantattun hanyoyi .
Maikifi ya ce akwai yiwuwar Najeriya zata cigaba da kasancewa cikin matsalar man fetur har sai an fara tace danyen man fetur a Nigeria .