A shirye nake na sanya hannu don zartar da hukuncin rataye Abduljabbar —Ganduje

Date:

Daga Maryam Ibrahim zawaciki

Gwamnatin jihar Kano ta ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje a shirye ya ke ya sanya hannu kan sammacin kashe malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

 

Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar, Lawan Musa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani kan hukuncin da aka yankewa Abduljabbar na hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan da wata kotun shari’ar musulunci ta same shi da laifin yin kalaman batanci ga Annabi S A W .

 

Musa ya ce gwamnan a shirye yake domin ganin ba a karya doka da oda a jihar kano ba, inda ya ce hukuncin da kotun ta yanke akan malamin gwamnatin jihar ta shigar da karar malamin, wanda hakan ke nuna babu wanda fi karfin doka.

Talla

“Ba za a bar kowa ya karya doka ba tare da daukar matakan da suka dace akansa ba.

“Mun kai shi (Abduljabbar) kotu, muka ba shi dukkan abubuwan da ya kamata domin ya kare kansa, kuma a yau mun gode wa Allah, kotu ta gamsu da hujjojin da muka gabatar a kansa, kuma ta yanke masa hukuncin da ya dace,” inji shi.

 

Musa ya kara da cewa: “Kamar yadda gwamna bai canza matsayarsa ba a al’amarin Hanifa, haka nan ma ba ta canza ba akan wannan lamari.

 

“Kun san akwai tsare-tsare da yawa da ya kamata a bi kuma mai girma Gwamna a shirye yake; da zarar an kawo masa wannan takardar, zai sa hannu domin zartar da hukuncin”. a cewar kwamishinan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...