Yadda tsadar man fetur ke kara tsananta a kano

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Masu ababen hawa na ci gaba da kokawa game da karancin man fetur da kuma tsadarsa a jihar Kano.

 

Wannan na zuwa ne bayan da jami’an tsaron farin kaya a jihar Kano suka yi wata ganawa da dillalan man fetur din game da karancinsa.

 

Gidajen mai da dama na sayar da shi kan fiye Naira 300 kowace lita, kuma kuma a rufe babu man.

 

Gidajen man da ake sayar da shi a farashin gwamnati kuwa sai mutum yaci kwakwa kafin ya samu saboda dan karan layi.

 

Talla

Game da wannan matsalar mai ne, hukumar tsaro ta DSS ta yi wata ganawa da dillalan man fetur a Kano cikin wannan mako.

 

Bayanai na cewa wasu dillalan man na boye shi ba tare da wani dalili ba.

 

Sai dai Shugaban kungiyar dillalan man IPMAN, reshen arewacin Najeriya, Bashir Dan Mallam, ya ce sun tattauna sosai da jami’an tsaron.

 

A farkon makon nan ne, majalisar dokokin Najeriya ta umarci kamfanin mai na NNPC da hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur da kuma dillalan man fetur da su yi duk mai yiwuwa cikin mako guda su kawo karshen matsalar man fetur, tare da tabbatar da sayar da man a farashi man rangwame.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...