Daga Rahama Umar Kwaru
Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara da Kotu ta Same shi da laifin yin batanci ga Annabi S A W kuma aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, yace roki kotu data sa gaggauta kashe kamar yadda aka yanke masa hukunci.
Sheikh Abduljabar ya bayyana hakan ne bayan alkalin kotun shari’ar musulunci dake zamanta a Kofar kudu karkashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

” Ni bazan daukaka kara ba Kuma bana so kowa ya daukaka kara a madadin na, sannan Ina kira ga kotu data ba da damar a gaggauta kashe domin nasan zan je wajen ubangijina a matsayin madaukaki”. inji Abduljabbar
” Ina sanar da dalibai na su yi hakuri su karbi wannan hukuncin wanda aka chanza hujjojina, saboda nasan ni dai kare ma’aiki na yi kuma idan aka yanke mun wannnan hukuncin zan je wajen ubangijina a matsayin madaukaki”. A cewar Abduljabbar
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa kotun ta yankewa Abduljabbar hukuncin kisa ne ta hanyar rataya da kwace masallatansa guda biyu da Kuma kwace litattafansa tare kuma da bada umarnin hana Sanya hotunan sa ko karatun sa a duk wasu nau’in kafafen yada labarai.