Yayin da ake ci gaba da zama a kotun shari’ar musulunci dake kofar kudu, yanzu haka mai sharia Ustaz Ibrahim Sarki Yola, yace kotu ta tabbatar da cewar kalaman batanci da Malam Abduljabbar yayi ga ma’aiki a cikin karatun sa, shi ne ya kirkirar su domin shaidu da hujjoji sun tabbata a kotun sun nuna cewar babu su a cikin litattafan da yake fada.

DW sun rawaito haka kuma kotun tace masu gabatar da kara sun gamasar da kotu cewar hakika Malam Abduljabbar yayi kalaman batanci ga Manzon Allah,
Kuma kotu ta tabbatar da cewar shaidun da aka gabatar a kotu sun tabbatar Abduljabbar ne yayi wadannan kalamai dan cin mutumcin ma’aiki, sannan kotu kuma ta gamsu da dukkan shaidun.
Ana cigaba da karanto hukunci Yanzu haka