Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a jihar Rivers sun sake kalubalantar gwamnan jihar, Nyesom Ezenwo Wike, inda suka ce sun fi shi biyayya ga jam’iyyar.
Da ya ke jawabi yayin taron kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a Port Harcourt, babban daraktan kwamitin a jihar, Dakta Abiye Sekibo, ya ce yawancin wadanda aka hana tikitin takarar gwamna a jihar, ba su fice daga jam’iyyar ba kuma ba su yi dissolving ba.
Sekibo ya ce: “Idan har an hana mu tikitin zama gwamna, kuma har yanzu muna goyon bayan jam’iyyar da dukkan karfinmu, to mu ’yan jam’iyya ne, to shi fa, me ya yi tun bayan faduwa zaɓen fidda-gwani na PDP?

“Don haka mu ’yan jam’iyya ne, kuma mun fi mara mata baya. Wannan shi ne abin da ya bambanta mu da shi”
Shi ma da ya ke jawabi, Chairman na kwamitin yakin neman zabe na jihar, Sanata Lee Maeba, ya ce masu goyon bayan muradin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar sun shafe shekaru da dama suna jam’iyyar.
Maeba ta ce: “A nan na san kun gamsu cewa girman mutanen da ke wannan teburin ya yi daidai da sunan PDP.