Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta koka da yadda a yanzu ‘yan siyasa ke sayen katin zabe na dindindin, wato PVC, don yin magudi a shekara ta 2023.
Wannan bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da masu kada kuri’a a fadin kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar nan suka fito domin karbar katin zabensu. An dai fara bayar ne a ranar 12 ga Disamba kuma ana sa ran za’a ƙare a ranar 27 ga Janairu 2023.
Mukaddashin shugaban hukumar zabe ta INEC kuma kwamishinan kasa mai kula da babban birnin tarayya Abuja, Nasarawa, Kaduna da Filato Mohammed Haruna ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin kaddamar da shirin #VoteMatters na wata kungiyar sa ido kan zabe mai suna NESSACTION a Abuja.

Ya bayyana cewa a baya-bayan nan ne Hukumar ta kama wasu mutane biyu a jihohin Sakkwato da Kano da laifin mallakar PVC ba bisa ka’ida ba.
Haruna ya jaddada cewa a yanzu ‘yan siyasa suna sayen katin zabe, inda ya gargadi masu kada kuri’a da kada su siyar da katinsu Saboda illar da hakan ke ciki.
Ya ce, “Wasu daga cikin ku na sane da cewa a baya-bayan nan ne INEC ta yi nasarar hukunta wasu mutane biyu da aka samu da laifin mallakar PVC ba bisa ka’ida ba a Kano da Sakkwato. Don haka ina kira ga jama’a da su alkinta katin zabensu , su kiyaye , sannan ku tabbatar kun fita don kada kuri’u a ranar zabe domin ba za ku iya kada kuri’a ba, ba tare da PVC din ku ba.”