Daga Rukayya Abdullahi Maida
Yayin da Karancin Man Fetur a Kano, ke Kara kamari, inda ake sayar da lita guda a kan Naira 310-320, Hukumar Tsaro ta Kasa, ta gayyaci kungiyar dallalan man fetur mai zaman kanta, DPR da sauran masu ruwa da tsaki, inda ta umurce su da su gaggauta magance matsalolin da suka haifar da tsadar man.
Wani babban jami’in DSS da ba ya so a ambaci sunansa, ya shaidawa Majiyar Kadaura24 cewa an yi taron ne a ranar Litinin wanda ya dauki tsawon sa’o’i da dama tsakanin jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki a sha’anin man fetur a kano.
Ya ce, dillalan man a wurin taron gudun da DSS suka jagororanta sun bayyana matsalolin da suke fuskanta a lokacin da suke jigilar man daga sassan Najeriya zuwa Kano.
A cewa wani jigon kungiyar yace wasu daga cikin matsalolin da suke fuskanta sun hada da tsadar Man Fetur din, rashin ingantattun hanyoyi da ke haifar da lalacewar tayoyinsu akai-akai, da kin biyan su kudaden dako.

Ya ce dillalan man sun amince da magance karancin man a kano nan da kwanaki biyu masu zuwa, inda ya ba da tabbacin cewa za a magance farashin man ta hanyar sayar da shi a farashin gwamnati na Naira 186 ga kowace lita.
Hakazalika, Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, DPR, ta riga ta kafa wasu kwamitoci guda uku wadanda zasu rika santa ido a kan kayayyaki a Kano, wadanda za su fara aiki, a ranar talatar nan domin tabbatar da samar da man fetur din ga jama’ar Kano ba tare da yankewa ba.
Hukumar ta DPR, ta ce ta baiwa hukumar DSS tabbacin tabbatar da bin ka’idojin samar da mai ba tare da yankewa ba, wanda nan da ‘yan kwanaki masu zuwa Kano zata fita daga jerin jihohin da suke fuskantar dogayen layin masu ababen hawa a gidajen man.