Sau biyar ina yunkurin sasantawa da Wike – Atiku

Date:

Daga Maryam Abubakar Tukur

 

Dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce sau biyar yana yunkurin yin sulhu kan rikicin jam’iyarsu da gwamnan jihar Ribas Nyesom amma hakan ya ci tura.

 

Atiku Abubakar ya ce yanzu yana jiran bangaren su Wike ne don ganin sun kawo karshen rikicin da jam’iyyar tasu ke fama da shi.

 

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a yayin taron tattaunawa da ‘yan takarar shugabancin Najeriya da gidan talabijin din Channels, ya gabatar a ranar Lahadin karshen makon da ya gabata.

 

Atiku Abubakar ya ce “na same shi a Abuja sau biyu, na kuma same shi a Patakwal sau biyu, sannan kuma a Landan sau daya.”

Talla

Sai dai Atiku bai yi wani karin bayani ba dangane batutuwan da suka tattauna da Wike a ganawar da ya ce sun yi ba.

 

Ya ce yana zargin kansa kan yadda suka gaza shawo kan rikicin.

 

Sannan ya ce matsalar daga bangaren Wike take ba daga gare shi ba.

 

Takaddamar da jam’iyyar PDP ke fama da ita, ta soma asali ne tun bayan da Atiku abubakar ya zaɓi Ifeanyi Okowa , a matsayin mataimakinsa, bayan zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar ta PDPda ake gudanar a ranar Asabar 28 ga watan Mayun 2022.

 

Duk da yunƙurin da jagororin jam’iyyar suka yi na rarrashin Wike, har yanzu gwamnan bai nuna alamun ajiye kayan yaƙinsa ba, inda shi da sauran gwamnonin jam’iyyar hudu suka matsa lamba sai shugaban jam’iyyar ta PDP Iyorchia Ayu ya sauka daga kan mukaminsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...