Zan raba tallafin karatun digiri a jami’ar NOUN ga ɗalibai 220 kafin zaɓe — Sha’aban Sharada

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

 

Ɗan takarar gwamna a jihar Kano, ƙarƙashin jam’iyyar ADP, Sha’aban Sharada ya yi alkawarin ɗaukar nauyin karatun digiri na dalibai, ƴan asalin jihar a jami’ar karatu da ga gida, wato National Open University (NOUN).

 

Sharada, ɗan majalisar wakilai mai wakilta

Talla

r Kano Municipal, ya yi wannan alkawari ne a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a.

 

 

Saharada ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin ɗalibai 5 daga ko wacce Ƙaramar Hukuma, a cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, inda adadinsu ya kai 220 kenan.

 

Ya kuma yi alƙawarin aiwatar da wannan aiki kafin zaɓen 2023.

 

“Kafin zabe, Zan Dauki Nauyin Karatun Dalibai biyar (5) a kowacce Karamar Hukuma (44) na Jahar Kano har su Gama Degree na farko a National Open University…5×44 = 220 Students,” in ji Sharada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...