Idan na zama Gwamna koyar da Qur’ani zai zama dole a makarantun Firamare da sakandire a kano – Sha’aban ya fadawa Malaman Kano

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

 

Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar birni kuma dan takarar gwamna a jam’iyyar ADP Sha’aban Ibrahim Sharada ya gabatar da kudirin kafa cibiyar binciken alkur’ani ta kasa a gaban majalisar wakilai.

 

 

Sha’aban Sharada ya bayyana hakan ne a lokacin da yake sanar da malaman Kano aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar kano.

 

 

A cewar Sharada, za a gudanar da karatun farko da na biyu na kafa cibiyar nan da makonni masu zuwa.

Talla

 

Ya shaidawa malaman cewar cibiyar binciken kur’anin wadda ake sa ran za’a rika koyar da ilimin kur’ani, ana sa ran za ta kasance a Kano ganin cewa kano ita ce mafi yawan mahaddata Alkur’ani a Najeriya.

 

 

Dan takarar gwamnan ya bayyana cewa idan aka zabe shi gwamnan kano zai mayar da koyar da karatun kur’ani a makarantun firamare da na sakandire a kano dole, kasancewar yana da sha’awar bunkasa harkar ilimi.

 

 

Sha’aban Sharada ya bayyana cewa ya zama wajibi a gare shi ya bayyanawa malaman muradinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Kano tunda malamai na da matukar muhimmanci da kuma kasancewar su masu ruwa da tsaki wajen tafiyar da tunanin al’umma.

 

 

Daga cikin fitattun malaman addinin musulunci da suka halarci taron akwai babban limamin masallacin Alfurqan Dr Bashir Aliyu Umar, Sheikh Abdulgaffar Nasiru Kabara, Sheikh Lawal Abubakar Triumph, Dr Abdullahi Muhammad Getso, Sayyadi Bashir Tijjani Zangon Bare-Bari wadanda suka fito daga dukkan darikun Kano.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...