Ku tsaya tsayin daka domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kano -; Sarkin Kano ya fadawa Sabon CP

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR CNOL ya bukaci sabon kwamishina yan sandan jihar Kano CP Mamman Dauda da ya tabbatar ya tsaya tsayin daka wajen kare lafiya da dukiyoyin al’umma jihar kano.

 

Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin sabon kwamishinan yan sandan na jihar Kano CP Mamman Dauda yayin da ya ziyarce shi a fadar sa.

 

Cikin sanarwar da sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, yace Alhaji Aminu Ado Bayero yace jihar Kano jiha ce mai al’umma da yawa, dole ne sai sabon kwamishinan yan sandan da ma’aikatan sa sun kara himma wajen kula da rayukan al’umma.

Talla

Anasa jawabin sabon kwamishinan yan sandan na jihar Kano CP Mamman Dauda ya ce rundunar “yan sandan jihar Kano zata cigaba da kokarin ganin ta kula da harkokin tsoran jihar kano.

 

Ya kuma bude sabon offishin yan sanda dake kofar kudu a fadar Mai Martaba Sarkin Kano.

 

Haka kuma a wani ciganan Mai Martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi bakuncin shuwagabanin kungiyoyin dalibai jami’oin kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...