Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Kwamishiniyar Ma’aikatar harkokin mata da cigaban Jama’a ta jihar Kano Dr. Zahra’u Muhammad Umar, ta bayyana mai dakin gwamnan kano Farfesa Hasafat Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin wacce tayi fice cikin matan gwamnonin kasar nan, bisa kokarinta da kwazonta akan cigaban mata dake fadin jihar Kano.
Dr. Zahra’u Muhd ta bayyana hakane a ranar Alhamis a lokacin da take zantawa da manema labarai a wani bangare na kammala taron samun horo na kwanaki biyar, “Mai taken Shugabanci da al’amuran gudanarwa” Wanda ya gudana a birnin Santanbul na kasar Turkiya.
Kwamishiniyar ta nunar da cewa Farfesa Hasfat Ganduje, ita ce ta jagoranci Tawagar matan jihar Kano, ta kuma yi kokarin samarwa mata guraben aikinyi a Gwamnatin Dr. Abdullahi Ganduje.

Ta kara da cewa samun horon sanin makamar aikin na kwanaki biyar zai taimaka wajen samun ilimi dai zai taimaka wajen ciyar da ilimi da martabar mata gaba.
Cikin sanarwar da jami’ar yada labaran ma’aikatar mata ta jihar Bahijja Kabara ta aikowa kadaura24, tace Kwamishiniyar ta kuma bayar da tabbacin cewa zasu aiwatar abin da suka koya a lokacin samun horon, domin Cigaban Jihar Kano da Najeriya baki daya.
Ta kuma yabawa Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Farfesa Hasfat Ganduje, bisa rawar da suke takawa wajen ciyar da daga darajar mata zuwa babban mataki a Jihar Kano