Shugaban hukumar kula da harkokin wutar lantarki a Najeriya ta Nigerian Electricity Management Service Agency (NEMSA) ya ce sun rusa gine-gine kusan 5,000 da ke ƙarƙashin manyan wayoyin lantarki a faɗin ƙasar.
Aliyu Tahir wanda shi ne kuma babban jami’in lantarki na ƙasa, ya faɗa a yau Juma’a cewa tun 2017 aka ɗauki mataki tare da ba da umarnin rushe gine-ginen da ke ƙarƙashin wayoyin, kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ruwaito.
NEMSA ta ce akwai buƙatar gaggauta katse yankunan daga layin lantarki da kuma rushe su daga baya.

“A ɓangarenmu, mun bai wa kamfanonin rarraba lantarki umarnin sauke duk wani gini da aka yi a ƙarƙashin babban layin lantarki daga kan layin wutar, har ma da waɗanda suka tare hanya,” a cewarsa.
Tahir ya ƙara da cewa rushe gine-ginen na buƙatar himma daga waɗanda abin ya shafa, “kamar gwamnatin tarayya da ta jihohi”.