Gawuna ya gana da ACF a Kano,ya bayyana shirinsa na bunkasa jihar Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida
 Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a ranar Alhamis ya halarci zaman tattaunawa da kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) reshen jihar kano, inda ya bayyana musu shirinsa na ciyar da jihar kano gaba, idan har r al’ummar Kano sun zabe shi a matsayin Gwamna a 2023.
 A yayin zaman, dan takarar jam’iyyar APC ya bada tabbacin dorawa kan aiyukan gwamna ganduje da kuma kaddamar da sabbin ayyukan cigaba, ya kuma bukaci sauran ‘yan takarar da su guji yaudara a yayin yakin neman zabe.
 Gawuna ya bayyana cewa, zai kuma ci gaba da samar da ingantattun ababen more rayuwa na tsaro da aka sanya, domin ci gaba da mayar da Kano jihar mafi zaman lafiya a kasar nan.
 A cewarsa, gwamnatinsa za ta samar da yanayi mai kyau na jawo masu zuba jari don tabbatar da ci gaban tattalin arziki tare da samar da ayyukan yi ga matasa maza da mata.
Talla
 Sanarwar da babban sakataren yada labaran mataimakin gwamna ya aikowa kadaura24, yace Gawuna ya yi alkawarin ci gaba da inganta ayyukan noma ta yadda za a bunkasa noman abinci a jihar kano.
 Ya shaida wa ACF cewa zai fadada Kano don hana cunkoso tare da mai da hankali kan ilimi, kiwon lafiya, samar da ruwa da samar da muhalli mai inganci.
Wani sashi na taron
 Shugaban kungiyar ACF reshen Kano, Dr.Goni Faruk Umar ya godewa dan takarar jam’iyyar APC bisa halartar taron tattaunawar da aka gaiyace shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...