Gwarazan shekara: ARTV ta karrama wasu daga cikin ma’aikatan ta

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Hukumar gudanarwar gidan talabijin ta Abubakar Rimi ARTV sun karrama wasu ma’aikatan ta bisa kwazon da suka nuna a yayin aikinsu a wannan shekara ta 2023 da ke karewa.

 

Dama dai duk shekara hukumar gidan talabijin din takan zabo wasu daga cikin ma’aikatan ta daga sassa daban-daban na gidan don karrama su bisa kokarin da sukai a wanna shekara.

 

Da yake jawabi a wajen taron Kwamishinan yada labarai na jihar kano Com. Muhd Garba ya ce irin wadannan kuautata wa da ake yiwa ma’aikatan zata Kara musu kwarin gwiwa ta Kuma zaburar da sauran ma’aikata.

Talla

” Irin wannan karawa ma’aikata karsashi, don haka ina kira ga sauran ma’aikatu da suke karkashin Ma’aikatar yada labarai dasu yi koyi da irin wannan salon na ARTV domin inganta aiyukan su”. Inji Muhd Garba

 

Itama a nata jawabin shugabar gidan talabijin din Hajiya Sa’a Ibrahim ta ce ta kirkiro bada lambobin yabon ne shekaru 4 da suka gabata domin karawa ma’aikatan ta kwarin gwiwa.

 

Tace an bi hanyoyin da suka dace wajen zabo wadanda aka baiwa lambar yabon daga sassa daban-daban na gidan talabijin din, ta Kuma yabawa gwamnatin jihar kano bisa gudanar da take baiwa tashar.

 

Daga cikin wadanda aka karrama akwai wakilin Gidan Tv a ofishin gwamnan jihar kano Wato Abdullahi Hassan wanda ya zamo Gwarzon shekara cikin masu aike da rahoto da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...