Dukan dan garuwa ya jefa Mazauna Hotoro dake kano cikin matsalar ruwa

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 Al’ummar unguwar Hotoro Danmarke a jihar Kano sun fada matsalar ruwa sakamakon zanga-zangar da masu sayar da ruwa suka fara yi a yankin .
 BizPoint ta rawaito cewa masu sayar da ruwan sun yanke shawarar ne bayan da wasu mazauna yankin suka kai wa daya daga cikin mambobinsu dukan kawo wuka, saboda ya ki sayar da ruwa ga daya daga cikinsu.
 Wani mai sayar da ruwa, Malam Yahuza Lawan, wanda ya shaida lamarin ya ce sun yanke shawarar daukar matakin ne saboda wasu mazauna yankin sun lakadawa mambobinsu dukan tsiya.
 A cewar Lawan, mazaunin garin ya bukaci mai sayar da ruwan da lamarin ya shafa ya sayar masa da ruwan, shi kuma yace wani kwastoma zai kaiwa, amma ya dage sai an kai masa ruwa .
 Ya kara da cewa a lokacin da ya ki bin su saboda yana kan hanyarsa ta kai ruwa ga wani kwastomomin da suka riga suka biya kudinsu, sai suka fara lakada masa duka har suka raunata daya daga cikin idonsa.
 Lawan ya kuma yi zargin cewa mazauna yankin sun yi sanadiyyar mai sayar da ruwan ya rasa idonsa.
 “Yanzu haka yana asibiti ana jinyarsa Likitocin sun shaida mana cewa ya rasa idonsa sakamakon mummunan dukan da aka yi masa.
 “Saboda haka, mun yanke shawarar dakatar da sayar da ruwa a yankin, kuma tuni wasu daga cikinmu sun riga sun yi tafiyarsu gida yayin da waɗanda ke nan suka ƙi ci gaba da sayar da ruwa.
Talla
 “Dole ne mu yi zanga-zanga kan abin da ya faru da dan uwanmu. Membobinmu sun sha fama da cin zarafi, don haka ba za mu sake lamuntar hakan ba,” in ji Lawan.
 Shi ma Adamu Khalil mai sayar da ruwa ya shiga zanga-zangar, inda ya ce ya rufe wurin sayar da ruwan don shiga zanga-zangar.
 “Sun yi masa dukan tsiya ne saboda ya ki sayar musu da ruwa bayan da ya ce su jira shi ya kai ruwan ga wani kwastomansa wanda tuni ya biya kudinsa.
 “Mun dakatar da sayar da ruwa har sai an yi abin da ya dace. Mun ji cewa jami’an ‘yan sanda reshen Hotoro sun cafke babban wanda ake zargin, Muna so a yiwa dan uwanmu adalci.” Inji Khalil.
 Majiyar Kadaura24 ta lura da cewa zanga-zangar ta haifar da karancin ruwa a yankunan Danmarke, Hotoro Bayan Depot, Unguwa Uku Kauyen Alu da dai sauransu.
 Tuni mazauna yankin suka fara fara gani tasirin zanga-zangar, kamar yadda BizPoint ta lura.
 Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce zai binciki lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...