Daga Zakaria Adam Jigirya
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce masu gayyatarsa zuwa muhawara suna kokarin amfani da shi ne kawai don samun kudi domin shi mutum mai tarin jama’a.
Tsohon gwamnan jihar Legas ya bayyana haka ne a gidan Chatham da ke birnin Landan ranar Litinin, sa’o’i 24 bayan da ya yi watsi da wata muhawara da wasu ‘yan takara uku suka halarta a zaben shugaban kasa na 2023.

Da yake amsa tambayoyi daga masu sauraro a kan dalilin da ya sa ya yi watsi da muhawarar, Tinubu ya ce, “Ina ganin kaina a matsayin mutum mai mutane, Kuna so ku yi amfani da ni don samun kuɗi kuma na ce ki.”
Dangane da cece-kucen da ya shafi shekarunsa, makaranta da lokacinsa a kamfanoni masu zaman kansu, ya ce, “A tarihin gidanmu anhaife ni a ranar 29 ga Maris, 1952, Sannan, lokacin ban ma a raina cewar zan zama shugaban Tarayyar Najeriya ba, ballantana ma nace zan shiga siyasa.
“Ina da kyakkyawan tarihi har a makarantar jami’ar da suke tambaya a kai suje su tambaya, bata lokacin su kawai zasu yi domin komai yana nan a rubuce a watan maris din 1952 aka haife ni.
“Daya daga cikinsu ma an zarge shi da cewa ba dan Najeriya ba ne, bana irin wannan maganar.