Rundunar sojin Sama ta kashe ƙasurguman ƴan fashin daji da ke addabar jihar Zamfara

Date:

Daga Daga Maryam Ibrahim zawaciki

 

 

Rundunar sojojin sama ta Najeriya tace jami’anta sun samu nasarar hallaka wasu ƙasurguman ƴan fashin daji waɗanda ke addabar ƙauyukan jihar Zamfara.

 

Rahoton Jaridar PRNigeria ya nuna cewa an samu nasarar kashe ƴan fashin ne a wasu hare-hare da jiragen sojojin Najeriya suka kai a wasu ƙauyukan jihar Kaduna.

 

Waɗanda aka kashen a cewar rahoton sun haɗa da Jibrin Gurgu, da Isah Jauro da kuma wani da ake kira Tambuwal.

 

Talla

Sauran sun haɗa da Noti, da Bala, da Yunusa da kuma Burti.

 

Bayanin da jaridar ta samo ya ce an kai farmakin ne a wasu sabbin sansanonin ƴan fashin a yankin ƙaramar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.

 

Haka nan an kai wasu hare-haren a yankunan ƙananan hukumomin Igabi da Birnin Gwari.

 

Wata majiyar tsaro ta ce an ga dacewar kai harin ne bayan rahotannin da ke cewa an samu ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...