Aisha Buhari ta janye ƙarar da ta kai ɗalibi Aminu Muhd

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Rahotannin na tabbatar da cewa uwargidan Shugaban kasa Aisha Buhari ta janye ƙara da tuhumar da take yi wa ɗalibin nan Aminu Muhammad, kamar yadda lauyansa ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC Hausa.

 

Cikin wani saƙon tes, Barista C.K. Agu bai yi ƙarin bayani ba game da dalilin da ya sa Aisha ta janye ƙarar.

 

Matakin na zuwa ne bayan ɗalibin, wanda ke karatu a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, ya shafe kwana uku a gidan yari da ke Suleja bisa umarnin kotun.

Talla

A ranar Litinin ake sa ran ci gaba da zaman kotun don sauraron neman beli da lauyan Aminu ya yi a zaman ranar Talata da aka yi, wanda bai yi nasara ba.

 

Matar shugaban na zargin Aminu da ɓata mata suna saboda saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twitter maƙale da hotonta tare da cewa “ta ci kuɗin talakawa”.

 

Ƙungiyoyin kare haƙƙi da masu sharhi sun soki Aisha game da matakin da ta ɗauka bayan rahotanni sun yi zargin cewa sai da aka lakaɗa wa Aminu duka kafin gurfanar da shi a gaban kotun.

 

Kazalika, wasu sun soki matashin kan zargin da ya yi wa matar shugaban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...