Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Sarkin kabilar Igbo a nan Kano Boniface Ibekwe Ezedioranma, ya nada Shugaban Ma’aikatan jihar Kano Kuma shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati Alhaji Usman Bala Muhammad a matsayin jakadan zaman lafiya na kabilar Ibo mazauna Kano.
Nadin ya gudana da yammacin yau lahadi a filin wasa na Ado Bayero square dake unguwar sabon gari a yankin Karamar hukumar Fagge.

Dayake jawabi Bayan nadin shugaban Ma’aikatan Jihar Kano Alhaji Usman Bala Muhammad,ya bayyana cewar zaman lafiya da kulawar da Gwamnatin Kano ke bawa Sauran kabilu na daga cikin dalilan da Sarkin kabilar ta Ibo ya duba tare da bashi wannan sarauta.
2023: Siyasar Kano na kokarin shiga mawuyacin hali
Usman Bala Muhammad,ya Kuma Kara da cewar wannan sarauta zata Kara kawo hadin kai da zaman lafiya tsakanin sauran kabilu dake fadin kasar nan.

Yayin taron an kuma karrama Alhaji Abubakar Isah da kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Fagge Aminu Sulaiman Goro da sarauta.