Daga Rukayya Abdullahi Maida
Duk masu bibiyar al’amuran yau da kullum musamman wadanda suka danganci siyasar kano, sun san yadda yanayin siyasar ya fara yin zafi tun lokacin da aka fara tun karar zaɓen 2023.
A yan kwanakin nan al’amarin na neman sake dawo wa sabo, musamman idan akai la’akari da zafafan kalamai da shugabannin manyan jam’iyyun na APC da NNPP suke yi, wanda kuma cigaba da yin irin wadannan kalamai ka iya tunzura magoya bayan kowanne bangare.
A ranar larabar da ta gabata a garin Gaya ya yin kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar APC, Shugaban jam’iyyar na jihar kano Hon. Abdullahi Abbas ya yi wasu kalamai wadanda suka ɗauki hankulan al’umma ba a Kano kadai ba har da kasa baki daya.
” Duk da ance in daina fada Amma za sake fada ko da tsiya ko da tsiya-tsiya kai ko ana ha maza ha mata sai mun ci zaɓen shekara ta 2023″ inji Abdullahi Abbas

Babu shakka wadannan kalamai basu je kunnuwan yan jam’iyyar NNPP da dadi ba, hakan tasa a wajen wani taro na masu ruwa da tsakin jam’iyyar aka jiyo shi ma Shugaban jam’iyyar ta NNPP Hon. Umar Haruna Doguwa ya yi makamantan kalaman na shugaban APC.
” Tun da Kun ce ko da tsiya ko da tsiya-tsiya sai kun ci zaɓe to mu ma mun shirya domin mun tanade ku, ayi tsiya-tsiyar komai ta fanjama fanjam, Kuma kowaye mutum idan yace mana kule zamu ce masa chass “. Inji Umar Doguwa
Babu shkka duk mai kishin kano idan yaji ana irin wannan musayar zafafan kalaman dole hankalin sa ya tashi, musammam ma idan kaji shugabanni ne ke wadannan kalamai , tabbas akwai fargaba a cikin harkar.
Akwai bukatar Malamai da sarakuna da Hukumomin tsaro su zaunar da wadancan shugabanni da su guji irin wadancan kalamai domin babu abun da zasu haifar a kano idan ba tashin hankali ba.
Yanzu haka sakamakon wadancan kalamai na shugabannin manyan jam’iyyu a Kano, wasu matasa sun fara furta abubuwa masa dadi tare da Shan alwashi wanda hakan barazana ce sosai ga al’ummar jihar kano baki daya.
Ya dai kamata masu ruwa da tsaki su takawa lamarin burki ko dan cigaban zaman lafiyar al’ummar jihar kano.