Sanatan Kano ta Tsakiya: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke takarar Danburan a PDP, ta tabbatar da Laila Buhari

Date:

Daga Umar Ibrahim

 

Kotun daukaka kara a Kano ta soke takarar Sanata Danburam Nuhu da jam’iyyar PDP ta yi a matsayin dan takarar Sanata a Kano ta tsakiya.

 

Don haka, kotun ta amince da zaɓen fidda-gwani da jam’iyyar ta gudanar, ƙarƙashin shugabancin Shehu Sagagi, wanda ya fitar Laila Buhari a matsayin ƴar takara.

Talla

A ranar 26 ga watan Satumba ne wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta yi watsi da karar saboda rashin hurumin shari’a, bisa hujjar cewa an shigar da karar ne a Kano maimakon Abuja, sabanin tsarin majalisar shari’a ta kasa NJC kan al’amuran da suka shafi kararraaki kafin zaɓe.

 

Amma a hukuncin da mai shari’a Ita Mbaba ya yanke a jiya Laraba, kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da kotun ta yanke, inda ta ce ta yi kuskure wajen yin watsi da karar a kan wannan batu.

 

A yayin da take sauraren wata babbar hujja kan cancantarta kamar yadda aka shigar da ita ta hanyar sammaci, kotun ta ce a wani batu na gabanin zabe, za a yi amfani da hukuncin babbar kotun tarayya da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (1999) da aka yi wa kwaskwarima akan manufofin NJC, wanda karamar kotu ta dogara da shi.

 

Daily Nigerian ta rawaito kotun ta umarci INEC da ta cire sunan Damburam tare da maye gurbinsa da na Laila Buhari.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...