An yanke hukuncin ɗauri kan Uba da ya yi wa ɗiyarsa fyaɗe tare da abokinsa

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Kotu a jihar Legas ta yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan wani uba da ya yiwa diyarsa fyaɗe tare da abokinsa.

 

Uban da aka bayyana sunansa da Adewale Ibitoye da abokinsa Moses Oruke sun rinƙa yiwa ɗiyarsa mai shekara 14 fyaɗe har ta kai ga su sun yi mata ciki.

 

Alkaliya Abiola Soladoye ta yanke musu hukuncin ne bayan kotu ta tabbatar mutanen biyu sun aikata laifin da ake zarginsu da shi.

Talla

Alkaliyar ta yi alla-wadai da wannan kazamin cin zarafin kan ɗiyar da mutum ya haifa, la’akari da yadda suka rinƙa lalata da yarinyar na tsawon lokaci babu tausayi.

 

Yarinyar ta shaidawa Kotu cewa uban nata bayan shafe tsawon lokaci yana yi mata fyaɗe, sai aka kai gaɓar da ya miƙa ta ga abokinsa da sunan wai shi ne sabon mijinta tare da karɓar kwalbar giya.

 

Alkaliyar a kotun da ke sauraron kararraki kan cin zarafi da lalata ta bukaci a sanya sunayen mutanen a kundin rajistar kotun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...