Kotu ta umarci INEC da ta dawo da yin rijistar katin masu zaɓe

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

A yau Talata ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta gaggauta dawo da rajistar masu kada kuri’a (CVR) har zuwa kwanaki 90 kafin zaben 2023.

 

Mai shari’a Inyang Ekwo, a cikin hukuncin da ya yanke, ya kuma umurci hukumar ta INEC da ta tabbatar da cewa ba a hana ƴan ƙasa da su ka cancanta damar samun katin zaɓe a zaɓe mai zuwa ba.

 

Mai shari’a Ekwo ya ce alhakin da tsarin mulki ya rataya a wuyan alkalan zaɓen ne su samar da isassun tanadin gudanar da zaben kamar yadda dokokin Nijeriya su ka tanada.

Talla

“Shari’ar masu shigar da kara ta yi nasara bisa cancanta,” in ji alkalin.

 

NAN ya ruwaito cewa Anajat Salmat da wasu mutane uku sun maka INEC a matsayin wanda ake kara, a ƙara mai lamba: FHC/ABJ/CS/1343/2022.

 

A farkon sammacin da suka gabatar a gaban kotun, masu shigar da kara sun ce INEC ba za ta iya dakatar da CVR ba sabanin yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

 

Sun bukaci kotun da ta umarci alkalan zaben da su ci gaba da gudanar da atisayen kamar yadda dokar kasar ta tanada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...