Ganduje ya sanya hannu a dokar Masu bukata ta musamma ta Kano

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu a sabuwar dokar masu bukaci ta musamman wadda ta bada damar Samar da hukumar Masu bukata ta musamman.

 

Gwamnan ya Sanyawa dokar hannu ne yayin taron majalisar zartarwar ta wanann makon wanda ya gudana a gidan gwamnatin jihar kano.

 

Da yake jawabi bayan Sanya hannu a dokar gwamna Ganduje yace an samar da dokar ne domin inganta Rayuwar masu bukata ta musamman, ta hanyar fitar da tsare-tsaren yadda za’a gudanar da aikin inganta Rayuwar su.

 

” Wannan doka da muka samar babu Shakka zata yi tasiri wajen ingantawa da magance matsalolin da masu bukata ta musamman suke fuskanta, Amma Muna fatan hukumar da za’a Samar zata lalubo hanyoyin da zasu inganta rayuwar su”.

Talla

Yace Mai bukata ta musamman shi za’a sa a matsayin Shugaban Wannan hukuma, saboda shi yasan halin da yan uwansa suke ciki, Kuma a kunshin Shugabannin hukumar za’a Sanya dukkanin rukunonin Masu bukata ta Musamma dake jihar nan.

 

Dama mun hana barace-barace a kano, hakan tasa muka bada umarnin Sanya Masu bukata ta musamman cikin daliban da za’a koyawa sana’o’i a cibiyar koyar da sana’a ta Aliko Dangote dake nan Kano, Kuma Muna fata ita ma Wannan sabuwar hukumar zata taimaka mana wajen tabbatar da hana barace-barace a jihar kano “.

 

 

Kafin Sanya hannu aka wannan dokar sai da majalisar dokokin jihar kano ta aikin ta akai kuma ya amince da ita sannan ta turowa gwamnan Kano domin Sanya hannu akan dokar.

 

Yayin Zaman majalisar zartarwar na wannan makon gwamna Ganduje ya Sanyawa dokokin kimanin goma Sha daya hannu bayan amincewa da su .

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...