Buhari zai ƙaddamar da sabbin takardun ƙudi ranar Laraba

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da sabbin takardun kuɗin ƙasar da aka sake wa fasali ranar Laraba.

Gwamnan babban bankin ƙasar Godwin Emefiele ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Talata a wajen taron kwamitin tsare-tsaren kuɗi.
Mista Emefele ya ce babban bankin ƙasar ba zai sauya ranar ƙarshe da ya saka na mayar da tsoffin kuɗin zuwa bankunan ƙasar domin sauya su da sabbin takardun kuɗin ba.
Talla
Ya ƙara da cewa shugaban zai ƙaddamar da sabbin takardun kuɗin a lokacin taron majalisar zartarwa na ƙasa.
Tun da a ranar 26 ga watan Oktoba ne dai gwamnan babban bankin ƙasar ya sanar da cewa za a sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar, inda ya ce sabbin kuɗin za su fara yawo daga ranar 15 ga watan Disamba, inda za a ci gaba da kashe su tare da tsoffin kuɗin har zuwa ranar 31 ga watan Janairun 2023, lokacin da za a daina karbar tsoffin ƙudin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...