Jam’iyyar APC Ta Nemi Goyon Bayan Baki Mazauna Jihar Jigawa

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar Jigawa a tutar jam’iyyar APC Alh. Umar Namadi dan Modi wato Ibrahim Auwal Dutse ya bukaci baki mazauna jihar jigawa da su bada hadin kai da goyan bayan su domin samun nasarar jam’iyyar APC a zaben shekarar 2023 dake tafe.

 

Shugaban kwamatin Ibrahim Auwalu Dutse yayi wannan kiran a lokacin daya ziyararci shugabannin kungiyar baki mazauna Unguwar Jigawar Tsada dake Dutse, babban birnin jihar.

Alhaji Ibrahim Auwalu Dutse yace sun ziyarce su ne domin tattaunawa da kuma tuntuba don samun nasarar Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

 

Talla

Tun farko a jawabin sa, Shugaban kungiyar mazauna baki na Unguwar Jigawar Tsada, Mallam Isyaku Sa’adu Dan Batta, ya ce sama da shekaru 10 a jihar Jigawa, wata jam’iyya ba ta taba neman hadin kansu ba sai wannan lokacin, bisa jagorancin Ibrahim Auwalu Dutse.

 

A cewar sa, ya zama wajibi su bada tasu gudunmawar domin cimma burin da aka sanya a gaba.

 

Ya kuma bukaci dukkanin baki mazauna jihar jigawan dasu bada cikakken hadin kai da goyan bayan su domin ci gaban kasa da kuma Jihar baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related