Kwankwaso ya Nada Sheikh Aminu Daurawa da Wasu Malamai Limaman Masallacin Juma’a na Gidansa

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

An nada Shahararren malamin addinin musuluncin nan na Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a matsayin babban limamin masallacin Juma’a wanda Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso ya gina.

 

A cikin wata sanarwa da gidauniyar Kwankwasiyya Development Foundation ta fitar tare da hadin gwiwar Sanusi Bature Dawakin Tofa da Dokta Yusuf Ibrahim Kofar mata, Daurawa, tare da wasu fitattun malaman addinin Islama guda bakwai an sanar da nada su a matsayin Limamai da mambobin kwamitin gudanarwa na Masallacin Juma’ar dake a Miller road, a unguwar Bompai a Nasarawa GRA, Kano.

Talla

Sen. Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP ne ya gina masallacin a karkashin gidauniyar sa ta agaji mai suna (Kwankwasiyya Development Foundation) kuma ya bayar da gudunmuwar ga jama’a ya ce an yi aikin ne domin ya zama sadakatujjariya ga mahaifinsa marigayi Alh. Musa Kwankwaso, Majidadin Kano wanda ya rasu a ranar 24 ga Disamba, 2020.

 

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

 

Wadannan sune sunayen jerin limaman Masallacin Juma’a na Alh. Musa Kwankwaso da Kuma bambobin hukumar gudanarwar addinin Musulunci ta Amana Islamic Centre, Kano.

 

1. Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa (Babban Limami kuma Shugaban Cibiyar).

 

2. Sheikh Sadiq Isa Abdullahi (Imam)

 

3. Sheikh Gwani Baffa Ite (Imam).

 

4. Sheikh Bazallah Nasir Kabara (Imam)

 

5. Dr. Sani Ashir (Mamban kwamitin).

 

6. Dr Muhammad Khamis Hussain (Sakatare kuma memba)

 

7. Sheikh Nura Abdullahi Salihu (Dan Majalisar).

 

8. Malam Ashir Nata’ala (limamin kamsusalawat).

 

sanarwar ta bayyana cewa masallacin mai suna Alh. Musa Kwankwaso an kaddamar da shi ne da Sallah juma’a a ranar Juma’a 21 ga Oktoba, 2022 yayin da Amana Islamic Centre za a kammala tare da kaddamar da ita a shekara mai zuwa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...